You are here
Home > Sashin Hausa >

Za A Ci Gaba Da Samun Ƙarin Farashin Man Fetur- Buhari

104 Views

A jiya Litinin ne Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya buƙaci ‘yan ƙasar da su yi tsammanin ci gaba da samun ƙarin farashin man fetur, yana mai cewa mutane za su riƙa siyan man fetur da tsada a daidai lokacin da farashin ɗanyen man fetur ke ci gaba da farfaɗowa a kasuwar duniya.

Ya kuma bada hujjar ƙarin kuɗin wutar lantarki, wanda ya haifar da ƙarin damuwa a tsakanin ‘yan Najeriya.

Shugaban, wanda ya bayyana haka a yayin Taron Duba Ƙwazon Ministoci na Shekarar Farko da aka yi a Ɗakin Taro na Fadar Shugaban Ƙasa, ya ce: “Annobar COVID-19, wadda ta shafi tattalin arziƙin duniya, ta tilasta mu mu yi wasu gyare-gyare waɗanda za su haifar da raɗaɗi a farko, amma kuma sun zama wajibi don amfaninsu na dogon zango.

“Kamar yadda kuka sani, lokacin da farashin man fetur ya faɗi a lokacin da ake tsaka da dokar zaman gida a duniya, mun cire tallafin man fetur, ta yadda masu amfani da man fetur suka samu sauƙi.

“Kowa ya yi maraba da wannan. Kodayake tasirin bada tallafi shi ne farashin man fetur zai sauya da canje-canjen kasuwar duniya. Wannan yana nufin, yayinda farashin man fetur ke ci gaba da farfaɗowa, za mu samu ƙari a farashin man fetur”, in ji shi.

Shugaba Buhari, wanda ya samu wakilcin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbjo, ya ci gaba da cewa: “Akwai mummunan tasiri idan gwamnati ta ci gaba da bada tallafi a farashin man fetur. Na farko, hakan yana nufin a dawo lokacin da ake bada tallafi mai tsada.

“A yau kuɗin shigarmu ya yi ƙasa da kaso 60%, ba za mu iya biyan tallafin ba. Hatsari na biyu shi ne yiwuwar dawowar layuka a gidajen mai, wanda abin godiya ne, hakan ya zama tarihi a ƙarƙashin wannan gwamnati”.

“A yanzu ‘yan Najeriya ba sa bin dogayen layuka kawai don su sha mai, kuma a farashi mai matuƙar tsada. Haka kuma, kamar yadda na nuna a baya, ba a yi tanadin bada tallafin man fetur ba a kasafin kuɗin 2020 da aka yi wa kwaskwarima, saboda ba za mu iya biya ba, indai ana buƙatar ware kuɗaɗe masu kauri ga lafiya, ilimi da sauran kayayyakin more rayuwa. A yanzu ba mu da zaɓi”, ya ƙara da haka.

Leave a Reply

Top
%d bloggers like this: