You are here
Home > Sashin Hausa >

Shugaba Buhari ya faɗa tarkon maƙiya – Abdulkarim Daiyabu

113 Views

Najeriya ta shiga tsaka mai wuya, gaba siyaki baya damisa. Ko dai mu kwato Muhammadu Buhari daga hannunsu a sami zaman lafiya ko su rabashi da Allah, su rabashi da kowa, kowa yayi takansa.


Daga lokacin da ‘yan uwanka na jini suka yi tarayya da makiyan ka, makiya Allah, makiyan bayin Allah amma kanuna kai, kafi amincewa dasu fiye da kowa, baka neman kowa ko sauraron kowa sai su da wadanda suka hadaka dasu, har kowa ya gane haka, duk wanda yace zai dogara da kai, ai shi ne ya yaudari kansa.

Tattalin arziki da tsaro da siyasa duk sun rushe. Babu wanda yasan inda aka dosa. Daga barayin gwamnati sai bokaye sai ‘yan kungiyar asiri, fajirai, kadai sune suke amfana da bala’in da ake ciki.


Wadanda duk yawansu, gaba daya basu fice su miliyan biyar zuwa goma ba, cikin mu miliyan dari biyu ko fiye (200m) amma suna nema sufi karfinmu saboda mun daka ta tasu. Idan Buhari ya taba gina sabuwar matatar mai cikin kasada shekaru uku (3) a matsayinsa na ministan mai, karkashin mulkin Obasanjo na soja, gashi yanzu Buhari shi ne shugaban kasa, mai cikakken iko, kuma shi ne babban ministan mai, amma ya kasa gyara matatun mai da muke dasu, balle ya gina sabuwar matatar man, mu huta da bala’in tsada ta shigo da tataccen mai da dangoginsa?Adnairax

Lallai da walakin, goro a cikin miya! Babu wata kasa da take da mai da matatun mai amma take shigo da tataccen mai sai Najeriya, saboda lalacewar shugabanci da zalunci. Babu wata kasa da take da arzikin Najeriya da sojoji da ‘yan sanda da DSS da NIA da customs da immigration da duk abinda ake kira jami’an tsaro amma babu tsaro a kasar.

Babu wata kasa da sojoji suka rusa mulkin dumokaradiyya suka maye guraben ‘yan siyasa farar hula aketa binsu a haka, har ya kai ga sojoji biyu; wanda yayi mulkin soja, ya soke zabe mafi inganci, ya dasa wanda ba dan siyasa ba ya zama shugaban kasa ba tare da zabe ba, ya hada kai da sojan da yake mulki suka fito da dan uwansu soja da aka daure, rai da rai, daga kurkuku suka yafe masa, suka kakaba mana shi, ya zama shugaban kasa na farar hula, mai cikakken iko.

Ina ‘yan siyasa farar hula masu rakadin dumokaradiyya? Hatta dan uwan wanda suka kakaba mana, na kabila da bangare da addini sai da ya gargadi mutane, kada a kuskura a rantsar da sojan da aka fito dashi daga kurkuku suka kakaba mana ya zama shugaban kasa, shugaban sojojin Najeriya dan kungiyar asiri ne! Sai gashi an shiga wani irin yanayi na Boko Haram da yin garkuwa da mutane domin kudin fansa. Yayi laifukan tsigewa 125 aka kasa tsige shi sai shi ne ya rika tsige shugabannin majalisar Dattijai da ta tarayyar kasa.

Kamar dai yadda nasha fadawa ‘yan siyasa, tun daga lokacin da aka yiwa Buhari juyin mulki aka fara rusa darajar naira da matatun mai, aka kara kudin mai da muke amfani dashi a Najeriya, aka rusa NEPA da masana’antu da NITEL da Nigeria Airways da Nigeria Railways da duk ababen more rayuwa da na tattalin arziki da ilimi da siyasa da zaman lafiya, aka fara horon matasa da zasu taimaka a cigaba da rusa Najeriya da ‘yan siyasa farar hula.

Aka wayi gari kusan duk dukiyar kasar ta zama mallakar sojoji da suka yi mulki da wadanda suka gurbata da wadanda suke juya musu dukiyar da suka sace mana. Ai Buhari ya taba sawa an bude ma’ajiyar kayan abinci da ‘yan kasuwa suka boye, aka sayar akan farashi mai rahusa, ya taba sawa a dauko Umaru Dikko daga gudun hijira a Ingila.

Yanzu mafiya yawan masu laifukan da su ka fi na wancan lokacin suna nan Najeriya wasu ma suna kewaye da shi, me zai hana a kama su a kwato duk abin da kowa ya mallaka ba ta hanyar gaskiya ba? Menene aikin hukumar shari’a da jami’an tsaro? Mene amfanin mulkin idan ba za’a tsare rayuka da lafiya da dukiya da mutunci da addini na kowanne dan kasa da baki, mazauna cikinta ba?

Duk wadanda aka zaba da wadanda aka nada da makusantansu da iyalansu da ‘ya’yansu da abokansu wacce irin rayuwa sukeyi? Kazamar dukiya da suka mallaka idan ba gada su ka yi daga mahaifansu ba wajibi ne sai an kwato mana duk abinda kowa ya mallaka an baiwa kowannen mu hakkinsa.

Tun daga gidaje wadanda suke ciki da wadanda ‘ya ‘yansu da ‘yan uwansu suke ciki da rukunin gidaje na haya (housing estates) da kudi na gida dana waje da hannayen jari a bankuna da kamfanoni da masana’antu da suke karkashin kulawar wasu mutane da sunan PLC, gida da waje da dukkan hakukuwanmu da suka danne mana.

Duk duniya babu inda aka taba samun wanda bashi aka zaba ba, ko yakin neman zabe bai taba zuwa ba amma yafi shugaban kasa iko. Idan ma rashin lafiya da Buhari ya kamu da ita ne yayi tsananin da ba zai iya tunawa da duk alkawuran da yayi aka zabe shi ba menene amfanin wadanda aka zabesu tare da shi? Menene amfanin wadanda aka nada? Menene amfanin ‘ya’yan ‘yan uwansa da suka hana kowa yaje kusa dashi sai su isu?

Maimakon su kwatanta abinda ya faru a Cuba, zamanin Fidel Castro da bashida lafiya dan’ uwansa ya gudanarda mulkin, dai dai da yadda shi, Fidel Castro din yake gudanarwa, komai yatafi dai dai, amma a Najeriya sai akasin na Cuba? Saboda irin tasirin makiyansa, makiya Allah makiya bayin Allah?

Ko wadan da basuyi zamani da tsofaffin shugabannin farar hula ba irinsu Prime minister, sir, Abubakar Tafawa Balewa da Premier, sir, Ahmadu Bello Sardauna Sokoto da ministocinsu, irinsu, Baba Ribadu da Maitama Sule da sauransu sun karanta ko sunji labari, har suka gama mulkin ko akayi musu juyin mulki babu abinda suka mallaka sai gidan kwana a garinsu sai kima da mutunci. Babu loot, a cikinsu

Haka Shehu Aliyu Shagari da Malam Adamu Ciroma da Binyamunu Usman. Hatta a sojoji; Yakubu Gowon da Murtala Muhammad me suka mallaka? Inbanda titina da kadarorin gwamnati da ake sa sunayensu? Babu wanda mukaji anyiwa lakabi da loot!!! Aziyarci gidajen duk sauran da sukayi juyin mulki, sukayi mulki da ministocinsu da sukayi mulkin tare da wadanda suka tarbiyyanta izuwa yanzu, aga bambancin a baiyane kafin kwamiti mai karfin shari’a ya fara aikinsa kowa yagane wallensa. Lalacewa, ba itace tayi kanta ba, wasune suka lalata. Haka gyara bazaiyi kansa ba, sai wasu sun gyara. Idan aka ki gyarawa ko aka kasa gyarawa to Allah ne kadai yasan abinda zai biyo baya. Allah ya bamu ikon gyarawa. Ameen, thumma ameen!

Abdulkarim Daiyabu, Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya (MOJIN) 08023106666, 08060116666.548

Leave a Reply

Top
%d bloggers like this: