You are here
Home > Sashin Hausa >

Babban Bankin Najeriya ya hana kudin shigo da madara kasar

169 Views

Babban bankin Najeriya, CBN, ya sanya madara da dangoginta cikin kayayyakin da ba zai bayar da rangwamen dala ga ‘yan kasuwa domin siyo su a kasashen waje ba.

Sai dai kuma bankin ya cire wasu kamfanoni shida daga cikin wadanda ya sanya wa wannan takunkumi.

A cikin wata sanarwa da babban bankin ya wallafa a shafinsa na intanet, ya ce “A wani bangare na kokarin kara bunkasa samar da madara da dangoginta a Najeriya, CBN ya zabi wasu kamfanoni da za a horar da ma’aikatansu yadda za a rinka samar da madara a cikin gida mai kyau da karko.”

Babban bankin ya zabi wasu kamfanoni da su kadai aka lamuncewa shigo da madara da dangoginta wadanda suka hada da:

Friesland Campina WAMCO Nigeria

Chi Limited

TG Arla Dairy Products Limited

Promasidor Nigeria Limited

Nestle Nigeria Plc (MSK only)

Integrated Dairies Limited

Wadannan kamfanoni da aka tsame daga cikin wadanda aka haramtawa shigo da madarar tuni suka fara samar da madarar gida a wani bangare na shirin inganta madarar gida da CBN din ya tsara.

Tun a watan Yulin 2019, gwamnan babban bankin Godwin Emefiele, ya tabbatar da shirin su na haramta shigowa da madara da dangoginta domin bunkasa samar da madarar gida a kasa.

Leave a Reply

Top
%d bloggers like this: