You are here

An fitar da wasu iyalai a jirgi saboda ‘warin jiki’

149 Views

An fitar da wasu iyalai a jirgi saboda ‘warin jiki’

Aika wannan shafi Email Aika wannan shafi Facebook Aika wannan shafi Twitter Aika wannan shafi Whatsapp
Image copyright AFP American Airlines planes
Image caption Iyalan sun maka kamfanin jigin gaban kotu saboda kalaman da aka yi game da addininsu da kuma bata musu suna
Wasu iyalai daga Michigan da aka fitar da su daga wani jirgin kamfanin Amurka a Miami bayan da wani ma’aikacin jirgin ya ce iyalan na da warin jiki, sun ce za su maka kamfanin gaban shari’a.

Cikin watan Janairun bara ne dai aka yi wa Yehuda Yosef Adler da matarsa Jennie da kuma ‘yarsu haka a wani jirgi da ya doshi Detroit.

Sun ce ma’aikatan jirgin sun yi ta furta maganganu game da addininsu na Yahudanci.

Kamfanin jirgin American Airlines ya ce matakin fitar da iyalan ba wai kan addininsu ba ne. Sun yi ikirarin cewa mutane sun koka kan warin jikin Mr Adler.

Karar, wadda aka shigar a Texas, ta bayyana bata suna da damuwa da kuma wariyar da aka nuna musu saboda addininsu.

Mr Adler ya ce iyalansa suna zaune a cikin jirgin, ko minti biyar ba su yi ba, sai wani ma’aikacin jirgin ya fada musu cewa akwai bukatar su fita daga cikin jirgin.

Kobe Bryant da ‘yarsa sun mutu a hadarin jirgi
Mutum 18 sun mutu a hatsarin jirgi a Sudan
Da suka bar jirgin kuma, Mr Adler ya ce ma’aikacin ya fada masa cewa matukin jirgin ya fitar da su ne saboda warin jikinsu.

Sun ce wani ma’aikacin jirgin “ya furta kalamai marasa dadin ji, inda ya fadawa iyalan cewa ya san Yahudawa suna yin wanka ne sau daya a mako.”

Hakan ya sa iyalan Adler suka rika tambayar ko mutane suna jin warin jiki na tashi. Sun ce sun tambayi mutum 20 amma ba wanda ya ce ya ji wani wari.

Mr Adler ya kuma ce sun yi wanka da safiyar.

An samar musu da daki a otal da abinci sannan aka sa su a jirgin da zai je Detroit washegari.

Amma babu akwatunansu saboda ba a ciro su daga cikin jirgin farko da suka hau ba.

Wata sanarwa da kamfanin jirgin ya aike wa Fox News ta ce: ” An bukaci iyalan Adler su bar jirgin bayan da fasinjoji da dama da kuma ma’aikatan jirgin suka koka cewa Mr Adler na warin jiki. An dauki matakin saboda walwalar sauran fasinjojin da ke cikin jirgin.

“Ba addini ba ne ya sa aka dauki matakin fitar da iyalan daga cikin jirgin ba.”

2020 BBC.

Leave a Reply

Top
%d bloggers like this: