You are here
Home > Entertainment >

An Ba Nazir Sarkin Waƙa Kyautar Motar Miliyan N50

85 Views

An ba fitaccen mawaƙin nan na jihar Kano, kuma tsohon Sarkin Mawaƙan Sarkin Kano, Nazir Muhammad Ahmad, da aka fi sani da Sarkin Waƙa kyautar mota G- Wagon 2019.

Fitaccen mawaƙin ya bayyana haka ne a wani gajeren faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Litinin.

A cewar mawaƙin, an ba shi wannan kyautar ne a yayin wani biki da ya je, inda aka ce masa an ba shi mota, kuma ya zaɓi wadda yake so.

“Jama’a, salamu alaikum dai farko, yanzu muka dawo daga dina, dina 2020, kodayake ni tun Disamba ma bara ban je dina ba sai wannan ta yau, ta yau Lahadi kenan.

“To an bada mota, sai aka bada motar, ni an bada motar sai aka ce min an ba ka mota sai na ce to na gode.

“Sai aka ce a’a, ai ba a gama ba, tsayawa za ka yi ka zaɓi wacce kake so. Duk motocin duniya in zaɓi wacce nake so? Sai na duba na ga a Najeriya wacce ce a kusa. Sai na ce to shikenan ba ka zurfafa fa ba ka takura ba, sai na ce a ba ni G-Wagon 2019”, ya bayyana haka a cikin faifan bidiyon.

Ya ci gaba da cewa: “Kun ga 2019 duk dinar da aka bada ita ai ta yi ko? An rufe ƙofa ba wata dina dai, sai dai wata ƙila nan da 2023 a ƙara irin wannan dinar.

“A bada motoci, kuma a motocin da G-Wagon 2019. Maganar liƙi ba a muku shi don watso kuɗi kawai ake, wullo su ake.

“An bayar. Yanzu muna nan mun zauna, ana jiran ta, kawai tana zuwa a buɗe mata ta shiga cikin ‘yan uwa, ta haɗu da ƙabila.

Auren Abdullahi Ɗan China da Zaituna. Wannan bara, ba mu je dina ba sai wannan. To dina da aka karɓi G-Wagon 2019 sai wannan”.

Binciken da Labarai24 ta yi ya nuna cewa mafi ƙarancin farashin G-Wagon 2019, motar da kamfanin Mercedes ke ƙerawa, yana farawa daga N50,548,794.

Leave a Reply

Top
%d bloggers like this: