You are here
Home > Sashin Hausa >

‘Yan kungiyar masu magunguna a Kano za su rufe shagunansu

361 Views

Daga MUSA DISO

Shugaban qungiyar masu saida magunguna, Nigerian Association of Patent and Propriotory Medicine Dealers (NAPPMED), reshen jahar Kano, Alhaji Husaini Labaran Zakari yace sun umurci ‘ya’yan kungiyarsu da su kauracewa bude shagunansu saboda irin cusgunawa da jami’an hukumar KAROTA take musu, wanda a cewarsa, basu da hurumin yin hakan a doka, ganin abinda ake musu ya zama rashin adalci a garesu shi yasa suka xauki wannan matakin.
Alhaji Husaini Zakari ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, yace bayan haka ma akwai wasu ma’aikata da ake ajiye wa a bakin kasuwa da haka kawai suke kama musu kaya. Duk da cewa ana gina musu kasuwa ta musamman da za su koma, amma ko yaushe ana kama kayan mutane ba tare da duba mai inganci ne ko mara inganci ba.
Ya yi nuni da cewa abin rashin jin dadi ba kwararru akan harkar ne suke yi ba,sunata hakuri akan hakan sai ya zama cewa yanzu KAROTA ta karbe aikin daga kwararrun da aka bai wa aikin.
A cewarsa, a nan Kano akwai kwamiti na haxin gwiwa da aka yi na karta kwana domin hana shaye-shaye da sai da kaya marasa kyau aka sa KAROTA ta zama daya daga cikin wakilai a ciki, da suka sami wannan dama dai suka kwace aikin ma har ta kai matsayin in mutane sun sayi kaya daga Kano za su fita da su ko za a shigo da su sai su tare wai sai sun kai ofishinsu anan ne za a ce kayan mai inganci ne ko mara kyau, sannan su baka ba tare da barin hukumar da take da hakkin yin abin suna yi ba. Shugaban na NAPPMED yace “hakan ya faru sau da dama muka kai wa KAROTA wasika a rubuce akan su rika barin masu alhakin kula da magungunan su rika yi amma sai shi shugaban KAROTA, Baffa Babba ya rubuto mana amsa cewa ba zai daina ba saboda suna da haqqi a ciki. Dan haka ma a kwanakin baya sun je wajen ajiyarsu na wani mutum an debi kayansa lokacin da waxanda suke da hakkin aikin suka zo suka ga abinda ya faru suka tabbayar kayan mai inganci ne bai kamata a dauke shi ba, a bar masa kayansa in ya zo sai a ga in ma akwai wani laifi da yayi sai a yi maganin abin.”
Daga karshe ya mika kokensu ga Mai Girma Gwamna jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, da ya sanya baki cikin wannan matsala ta su, wanda in ba haka, a cewarsa, “kasuwanci yana dab da mutuwa a jihar Kano.”

Leave a Reply

Top
%d bloggers like this: