You are here
Home > Sashin Hausa >

Yadda Boko Haram ta kashe sojojin Najeriya biyar a Borno

140 Views

Rundunar sojin Najeriya ta ce mayakan Boko Haram sun kashe sojojinta biyar a kusa da garin Jakana mai nisan kilomita 30 daga birnin Maiduguri na jihar Borno a ranar Laraba.

A wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta fitar a shafukanta na sada zumunta ta ce sojojin da suka mutu sun hada da Kanal da Kaftin da wasu sojojin uku a wani kwanton bauna da mayakan suka yi musu, a yayin da suke tafiya Damaturu daga Maiduguri.

Rundunar sojin ta ce tun da fari mayakan Boko Haram din ne suka yi kokarin kai hari sansanin sojoji na Bataliya ta 212 da ke Jakana ranar Larabar domin “satar kayan yaki da suke tsananin nema.”

Mayakan sun je ne da misalin 6.45 na yamma a motocin igwa bakwai kuma an fafata da su sosai a yayin da suke son kutsawa sansanin da karfi.

Sai dai sojojin Najeriyar sun fatattake su ta hanyar musayar wuta sosai.

Daga bisani ne mayakan suka “karaya bayan da aka lalata musu kayan yaki sosai tare da rasa wasu daga cikinsu, sannan kuma suka gudu ta Benisheikh da ke hanyar Damaturu – inda suka bar igwa dinsu daya da aka lalata wacce ga alama sun so zuba kayan da suka sata ne a ciki,” a cewar sanarwar.

Sojoji sun kwace kayayyaki daga wajen mayakan da suka hada da bindigar harbo jirgin yaki da roka biyu da bindiga kirar AK 47 biyu da alburusan bindiga kirar machine gun 15 da kuma alburusan bindiga mai carbi 15.

Babban hafsan sojin kasa na Najeriya Laftanal Kanal Tukur Yusuf Buratai ya jajantawa iyalan sojojin da suka mutu din wadanda ya kira “gwaraza.” Ya kuma sake jinjinawa sojojin kasar da ke yaki da kungiyar.

Kungiyar Boko Haram da ta IS a Afirka ta yamma ISWAP sun sha kai hare-hare a wuraren da ke tsakanin titin Maiduguri da Damaturu mai tsqwon kilomita 120 ko dai sansanin sojoji ko kasuwanni kamar Jakana.

Harsasan da aka kwace a hannun Boko Haram

A watan Disambar 2018 a kalla sojoji 13 mayakan ISWAP suka kashe a wani kwanton bauna da suka yi musu a kusa da kauyen Kereto da ke babban titin.

Mayakan sun kuma kai hare-hare da dama kan ababen hawa a titin inda suke kashe fasinjoji su kuma kona motoci.

Bayan shafe kusan shekara 10, mayakan Boko Haram suna ci gaba da kai hare-hare a Najeriya da ma makwabtanta irin su Nijar da Chadi da Kamaru.

Fiye da mutum 27,000 aka kashe kusan miliyan biyu kuma aka raba su da muhallansu a tashin hankalin.

Abin da ya kara tsananta tashin hankalin shi ne rabuwar kungiyar “ta’addanci” biyu a shekarar 2016 inda suka zama Boko Haram da ISWAP.

ISWAP ita ce wacce ta yi mubaya’a ga shugaban IS Abu Bakr al-Baghdadi.

Leave a Reply

Top
%d bloggers like this: