You are here
Home > Sashin Hausa >

Wace barazana ke tattare da manhajar FaceApp?

132 Views

Masu amfani da shafukan sada zumunta na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu kan manhajar FaceApp- manhajar da ke sauya hotunan fuskokin mutane ta nuna su da yarinta ko tsufa.

Dubban mutane na ta nuna sakamakon amfani da manhajar a shafukansu na sada zumunta.

Amma tun da manhajar ta bazu a ‘yan kwanakin nan, wasu sun nuna damuwarsu kan sharuddanta.

A ganinsu, kamfanin da ya samar da manhajar bai dauki bayanan masu amfani da ita da muhimmanci ba, amma kamfanin FaceApp ya ce ya cire mafi yawan hotunan daga rumbunsa na intanet sa’o’i 48 bayan dora su.

Haka kuma, kamfanin ya ce hotunan da masu amfani da manhajar suka zaba da kansu ne kawai yake aiki da su ba duka hotunan da ke kan waya ba.

Mece ce manhajar FaceApp?

Manhajar FaceApp ba sabuwa ba ce. Shekaru biyu da suka gabata aka fito da ita inda take iya sauya kalar fatar mutum.

Wannan ya jawo ce-ce-ku-ce sosai kuma ya ja aka sauke manhajar.

Manhajar na iya sauya dakakkiyar fuska zuwa mai murmushi. Kuma yana iya sauya kwalliya ma.

One of the artworks given a smile by Olly Gibbs
Image captionRumbun internet da Manhajar FaceApp ke amfani da shi a Amurka yake, amma ita kanta manhajar wani kamfanin Rasha ne ke da ita

Ana iya yin duka wannan ne tare da taimakon basirar na’urori wato Artificial Intelligence. Wasu bayanai na daukar hoton fuska sannan ya daidaita shi da wata basira da ke iya sauya kamanni.

Wannan na bayar da damar a sa murmushi ta hanyar motsa baki, da haba da kumatu don nuna kamar na gaske ne.

A ina matsalar take?

An nuna damuwa a baya-bayan nan lokacin da mai samar da manhaja Joshua Nozzi ya wallafa sako a shafinsa na Twitter yana cewa FaceApp na dora hotuna da dama na mutane daga wayoyinsu na hannu ba tare da izininsu ba.

Sai dai, wani mai bincike kan harkokin tsaron shafukan sada zumunta dan Faransa ya ce babu wata damuwa a tattare da amfani da manhajar.

FaceApp ta tabbatar wa da BBC cewa hotunan da masu amfani suka bayar da dama ne kawai manhajar ke amfani da su.

Ko masu amfani da manhajar sun san barazanar da ke tattare da amfani da ita?

Ga wasu, wannan ita ce babbar matsalar. Manufar manhajar ta tsare bayanan mutane ta nuna cewa ana iya amfani da bayanan wasu mutanen don aika musu da talla.

Masani a harkokin intanet Mista Walshe ya shaida wa BBC cewa an yi haka ne a wata hanya da ba lallai a gane ba.

Examples of FaceApp features
Image captionManhajar na iya sauya dakakkiyar fuska zuwa mai murmushi. Kuma yana iya sauya kwalliya ma

“Sharuddan amfani da FaceApp sun bai wa kamfanin damar yin duk abin da suka ga dama da hotunan masu amfani da ita, wanda abin damuwa ne amma ba abin mamaki ba,” in ji Dakta Murdoch.

“Kamfanoni sun san cewa kusan babu wanda yake karanta manufofin tsare bayanai don haka su kan sake abubuwa da yawa a cikin sharuddan ko da ba sa bukatarsu yanzu.”

Me FaceApp ke cewa?

Mista Goncharov ya fitar da wata sanarwa dake cewa FaceApp na daukar hotunan da masu amfani suka zaba.

“Ba ma daukar wasu hotunan,” a cewarsa.

“Za mu iya ajiye wa a rumbun mu.

“Dalilin hakan kuwa shi ne don gyara aikinmu da yadda mutane ke rububin manhajar: mun aso mu tabbatar da cewa masu amfani da manhajar ba su sa hoto daya sau da yawa ba.”

“Muna cire mafi yawan hotuna daga rumbunmu cikin sa’o’i 48.” a cewarsa.

Leave a Reply

Top
%d bloggers like this: