You are here
Home > Sashin Hausa >

Sakon WhatsApp zai iya kai mutum gidan yari

185 Views
Kafofin sadarwa na Intanet

‘Yan majalisar dokoki a Nijar sun amince da kudurin dokar hukunta ayyukan ta’adanci ta hanyoyin sadarwa na zamani.

Dan majalisa daga jama’iyyar MNSD nasara mai mulki Murtala Mamuda ya shaida wa BBC cewa “dokar za ta fara aiki nan da mako biyu idan Shugaba Mahamadou Issoufou ya sa ma ta hannu.”

Nijar na fama da hare-haren kungiyoyi masu tayar da kayar baya irinsu Boko Haram da makamantanta da ke yankin Sahel.

Sai dai wasu na fargabar irin wannan dokar za ta dakile ‘yancin fadar albarkacin baki a kasar.

Amma dan majalisar ya ce an kafa dokar ne da nufin dakile ayyukan batsa ga yara da ta’addanci da bata sunan mutane.

Gwamnatin Nijar na son kafa dokar ne kan abin da ta kira yadda mutane ke shiga intanet suna abin da suka ga dama da zai iya kawo tashin hankali da bata sunan mutane.

“Dole ana aiki da dokoki da za su kawo kwanciyar hankali da tsara rayuwar mutane”

“Yanzu duk wanda zai shiga kafofin sadarwa na intanet ko amfani da WhatsApp ya san akwai doka da ke kallonsa,” in ji Honarabul Mamuda.

Ya kara da cewa ba daidai ba ne ace akwai abin da ba shi da tsari da doka, Nijar ta yi latti domin kasashen duniya da dama sun yi irin wannan dokar.

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou

“Sai yanzu wadannan abubuwan Intanet suka zo a Nijar da suka hada da WhatsApp.”

“Aikin gwamnati ne ta kare kasa da saita mutane tare da kawo akida a kasa,” a cewarsa.

Duk wani aiki na bata kasa za a hana shi kuma za a hukunta duk wanda ya saba dokar da ke jiran amincewar shugaban kasa.

Da zarar kudirin ya zama doka, duk wanda aka kama da laifin yi wa wani kage ko sharri, to zai fuskanci hukuncin zaman gidan kaso.

Akwai ayar doka ta 31 da ta yi bayani game da dokar, wacce ta kunshi daurin wata shida zuwa shekara uku.

Sannan za a ci mutum tara ta kudi daga CFA miliyan daya zuwa daidai laifin da mutum ya aikata.

Ana ganin yana da wahala shugaban kasa Mahamadou Issoufou ya yi watsi da dokar da ke neman takawa kafafen sada zumunta birki.

Za a wallafa dokar a jaridu domin fadakar da al’umma game da ita.Leave a Reply

Top
%d bloggers like this: