You are here
Home > Sashin Hausa >

Red Cross ta Nisanta kanta da Boko Haram

119 Views

Kungiyar bayar da agaji ta nesanta kanta daga zargin bai wa kungiyar yan ta’addan Boko Haram agaji a yankin arewa maso gabashin kasar. Jami’in labaran kungiyar Red Cross ta duniya, da ke birnin tarayya Abuja, Aliyu Dawabe ne ya bayyana hakan inda yace basu taba nuna tausayi ko goyon baya ga wata kungiyar ta’adda ba. Dawabe ya kara da cewa yawancin ‘yan Najeriya ba su fahimci yadda ayyukan kungiyar agajin ya ke ba. Ya ce da ya ke ayyukan kungiyar agaji ya na tafiya ne kamar yadda Dokar Gudanar da Ayyukan Jinkai ta Duniya ta shimfida, sai wasu da dama ke ganin tunda Red Cross ba ta goyon bayan kowane bangare, to kamar ta na mara wa masu ta’addanci baya kenan. Daga nan sai ya ce ita kuwa wannan doka, ta bayar da umarnin cewa masu aikin agaji su gudanar da ayyukan ceto ga dukkan bangarori biyu masu fada da juna.

Kafin wannan dai, Kungiyar Red Cross ta sha fama da suka da caccaka cewa ta na nuna tausayi ga Boko Haram, wadanda aka ce ta na ba su magunguna da kuma gudanar da ayyukan duba lafiyar su. Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Mallaki manhajar AFRICAN MAESTRO Dan samun labarai da dumi dumin su: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.andromo.dev661623.app938722

Leave a Reply

Top
%d bloggers like this: