You are here
Home > Sashin Hausa >

Nijeriya zata fada cikin…..Dahiru Bauchi

117 Views

Babban malamin addinin Musulunci kuma jagorar kungiyar darika na kasa, Sheikh Dahiru Bauchiyayi tsokaci akan shirin gwamnatin tarayya na dakatar da almajiranci a kasar. Shehin Malamin ya kaulubalci gwamnati kan cewa har yaushe ne gwamnati za ta ciyar da masu bara su koshi alhalin tana fama da ma’aikatan ta. Ya bayyana cewa ana kokarin hana miskinai hanyar neman abincinsu domin wasu ta hanyar barar ne suke samun abun kai wa bakin salati. Dahiru Bauchi ya kuma ja kunnen gamnati kan cewa ta kiyaye domin kada ta janyo mumunan fitina a kasar. Ya kara da cewa idan har aka matsa toh za su yi addu’a kan su miskinan nan Allah Ya maida su matsayin masu hana barar, su kuma masu hanawa Allah Ya maida su matsayin miskinan kuma Allah zai . Yace “Wallahi aka hana bara ba a tanada musu abin da za su ci ba, masifar da za mu fada a kasar nan abin babu kyau. Su miskinan nan fa Allah Yana sonsu kamar yadda Yake son kowa, ba laifi suka yi wa Allah ba Ya maida su haka.

“A kiyaye, idan ba haka ba za mu jawo mummunar fitina a kasar nan. Idan kuma an matsa za mu yi addu’a su miskinan nan Allah Ya maida su matsayin masu hana barar, su kuma masu hanawa Allah Ya maida su matsayin miskinan kuma Allah zai amsa don haka a kiyaye.

YAKAMATA KA KARANTA: Red Cross ta Nisanta kanta da Boko Haram

“Yanzu ma muna cikin bala’in yunwa da matsuwa da damuwa a kasa, mun rasa inda za mu sa kanmu saboda rikicin zagin waliyyai da kafirta Musulmi da ake yi ya jawo fushin Allah a kan kasa. Mutane suna karkashe mutane ba gaira ba dalili, sun hana mu zama lafiya saboda Allah Ya yi fushi ana gaba da waliyyanSa, ana zagin amajiransu ana kafirta Musulmi. “Yanzu kuma ana so za a sake jawo mana wani babban bala’i na hana miskinai masu bara, ba a ba su abinci ba. Wannan abin da zai rikito da shi a Najeriya ya fi wanda muke ciki muni. Allah Ya shigar da wata mace wuta a Lahira saboda kyanwa, ta tare ta ba ta ba ta abinci ba, ba ta bar ta ta je ta nema da kanta ba har ta mutu, sai Allah Ya sa matar a wuta.”

Mallaki manhajar AFRICAN MAESTRO dan samun labarai da dumi dumin su: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.andromo.dev661623.app938722

Leave a Reply

Top
%d bloggers like this: