You are here
Home > Sashin Hausa >

KUSKUREN MALAMAI NA IYA JEFA QASA DA DUBBAN MUTANE GA HALAKA . ANNOBAR GARIN BAGADAZA DA TA AUKU A SHEKARA TA 1831ad=1246ah, kusan bata da banbanci da covid 19… Dr Zarewa

315 Views

Wannan annoba da ta faru a garin Bagadaza ta canza komai daga mahallinsa, sai da ta mayar da garin Bagadaza tamkar leda a cikin guguwa.
Ana iya cewa wannan annoba ita ce annoba mafi firgici da garin bagadaza ya hadu da ita a tsawon tarihi, wadanda Allah ya yiwa tsawon rai suka tsira daga wannan annobar sun jima suna ba da labarin irin barnar da wannan annoba ta yi.
A yanzu haka akwai wata kasuwa a garin Bagadaza da ake kira kasuwar Ja’ifa (kasuwar mussa), dalilin kiranta da wannan suna, shi ne cikar da tayi fal da gawarwaki lokacin wannan annobar, inda ba abin da ke tashi sai warin gawa.
Wannan annoba ta fito ne daga arewancin Bagdaza, a watan Yuli na 1830ad, gabanin isowarta Bagadaza mutan garin sun sami labarin bullar annobar a garin Tibriz na Iran, bayan wata biyu kuma sai ga labarin bullarta garin Karkuk.

TSARIN KILLACE MUTANE (Quarantine)
Jin haka ke da wuya sai sarkin Bagadaza Dawud Basha ya nemi babban likitan ofishin jakadancin kasar Birtaniya da ya fitar da tsarin Quarantine, (killece mutane don tsaron lafiyarsu) don dakile isowar cutar kasar ta Bagadaza, sai kuwa likitan ya aiwatar da wannan tsari na Quarantine, da kulle iaykokin kasar.

MATSAYAR MALAMAN ADDINI KAN WANNAN TSARI NA KILLACE MUTANE A GIDA, DA ILLAR DA TA HAIFAR.
Malamai masu fatawa na kasar a wannan lokaci sai suka bijire, da zummar cewa hakan ya sabawa shari’ar musulunci, suka hana sarkin garin Dawud Basha daukar duk wani mataki da zai dakile isowar annobar, hakan kuwa ya bawa falake daga Iran, da Kurdistan shigowa Bagdaza cikin kwanciyar hankali.

MAI ZAI FARU KUWA:
A cikin watan Maris na shekarar 1831ad, sai aka sami mutum na farko da ya kamu da annobar a garin Bagadaza, a yankin da yahudawa ke zaune masu kazanta, daga nana sai annobar ta ci gaba da ayaduwa a wasu yabkunan.
Wani mazaunin garin a wannan lokacin mai suna: Sulaiman Fa’iq ya ce: adadin gawarwakin da aka fitar zuwa bayan gari a karshen watan maris din sun kai 1000, zuwa tsakiyar watan afrilu kuwa sai da ya zama ana fitar da gawa kusan 3,000 a kowacce rana, daga bisani, su kansu ma’aikatan da ke rubuta adadin mamatan sai da ya zanto ba sauran ko daya.

MATSAYAR DA TURAWA DA KIRISTOCIN DAKE GARIN SUKA DAUKA A LOKACIN (IYA RUWA FID-DA KAI)
Ganin haka ke da wuya sai turawa da kiristocin da ke da alaka da su, suka maza suka killace kansu a gidajen su, bayan sun tanadi kayan masarufi, ya zama basa fitowa ko nan da can, basa cakuduwa da juna, in ma akwai abin da suke so daga waje sai dai su janyo shi da igiya, ko wasu abubuwa masu kama da filaya, sannan sai suyi masa hayaki don kashe kwayoyin cutar da ke tare da shi, kafin su yi anfani da shi, hakan ta sa ba a sami wadanda suka kamu da annobar ba a cikin su da yawa, wadanda ma suka kamu, sun harbu ne ta hanyar maguna da suke shiga wurinsu.

YANAYIN SAURAN MAZAUNA GARIN
Su kuwa sauran mazauna garin sai suka mika wuya suka ce sun sallamawa kaddara, annoba kuwa ta ringa girbe su matsanancin kisa, har sai da ta kai kimanin mutum 9,000 na mutuwa kullum.
Duk da cewa wasu ma ba annobar ce ta kashe su ba, masifar shiga firgici ne ya kasha su.

LABARIN WANI DAN MISHAN
Akwai wani dan mishan mai suna Groves dan kasar Birtaniya, wanda yake zaune a Bagadaza, ya kasance ya bude wata makaranta ta kiristoci marayu, da wannan annoba ta bullo, sai shugaban ofishin jakadancin kasar birtaniya ya ce ya kwashe yaransa su koma can kauyukan Basra don gudun kamuwa da annobar, sai Groves ya ki, ya ce ya dogara ga Allah, sai ya kulle gidansa shima, da kimanin mutum 12, a ciki.
Ya ce: daga gidan su akwai inda suke zama suna hango me ke faruwa a waje, sai da ta kai ana fitar da gawarwaki wurin 17,000, kowacce rana.

YANAYIN CIKIN GARI DA TITUNAN BAGADAZA A WANNAN LOKACIN.
Groves wanda ya wallafa littafi kan wannan annoba, ya ce: ta kai ba kowa a tituna face masu aikin fitar da gawarwaki, da masu kawo ruwa don wanketa.
Har sai da takai an rasa inda za a rufe gawa sai a gafen tituna, har ma a kan hanyoyin, da duk inda aka dan hangi fili, saboda cinkushewar da garin ya yi da kayayyaki da kuma gawarwaki.
Ya ce: har sai da ya zama mutane sun saba da mutuwa, ta yadda mutum dan uwansa zai mutu, zai birne shi ba tare da wata damuwa ba.
Daga nan fa lamari ya kara kamari har ya kai mutane na yanke jiki su fadi a kan tituna su kadai, ba wanda zai iya birne su, sai dai karnuka su zo su ci abin da za su ci kawai, wasu ma lokacin rai bai gama fita daga jikinsu ba.
Abin da ya fi komai tashin hankali a lokacin su ne kananun yara da suke ta faman kuka bayan mutuwar iyayensu mata. Baka iya rabe kukan na su da haushin karnuka.
Groves ya ce: abin da yafi bashi mamaki, shi ne yadda mutan Bagadaza suka matsanta wurin wanke gawa kafin a rufeta, a cikin wannan yanyi, alhali kuma kafin haka ba su damu da keta alfarmar Allah ba.
Sai da komai ya yi tashin gwaron zabi har likafani.

YADDA TA KAYA DAGA KARSHE:
Sulaiman Fa’iq ya ce: da yaga abin ya fara kazanta, tun lokacin ma, mutanen da suke mutuwa ba su fi 600 zuwa 700 ba a rana, sai ya je ya nemi izinin mahaifinsa, wanda bafaden sarki ne, cewa ya kamata su fita su bar garin don tsira da rayuwarsu, sai babansa ya ce, ya kai dana ai baya halasta a gujewa annoba, duk wadanda suk mutu ta sanadiyar guduwarsu sun yi sabo, don haka muyi zaman mu, in ma mun mutu mun yi shahada, wanda kuma ya tsira ya more.
Sulaiman ya yi kokarin gamsar da mahaifinsa yana mai kafa masa hujja cewa asalin wannan kuskuren na maluman da suka ki bawa sarki goyon bayan killace garin ne tun asali, kuma kai kasan ra’ayinsu ne kawai ba na shari’a ba, mahaifin ya gamsu, amma sai yace, duk da haka bazai yiwu in fita in bar sarki Dawud Basha ba, mahaifin ya ce shi ya tafi kawai, ya barshi, da yaje ya rayu takobin yan siyasa ta kashe shi, gara ya mutu ta wannan hanyar.
Sulaiman ya je ya debi yan gidansu ya fice da su can nesa da gari, ya zama duk bayan kwana 4 sai ya canza wuri, har dai Allah ya tseratar da su, ba wanda ya mutu a cikin su sai wadanda ke shiga cikin gari samo tsaki.
Bayan annobar ta lafa, sai Sulaiman ya maza ya shirya komawa gida, musamman saboda barayin da suke kusa da inda suke zaune, suke yiwa mutane kwace.
Ya ce: tun da suka fito basu hadu da koda mutum daya ba a hanyar ta su, har sai da suka kai gidajen kiristoci, sai ga wata mata ta leko, da ta gansu, sai ta koma ciki ta kira yan uwanta cewa su zo suga wasu mutane a raye, sai Sulaiman ya tanbayeta yadda aka yi suka tsira, tare da cewa babu koda mutum daya da suka hadu da shi akan titi?
Sai tace: tun lokacin da annobar ta fara yaduwa muka killace kan mu, kimanin mu 41, yanzu mun zama mu 43, an Haifa mana yara 2, kasancewar mun manta rabon da muga wani dan adam ya gitta, ganin ku yasa muka yi farin ciki, saboda hakan na nuna cewa annobar ta tafi,.
Koda Sulaiman suka isa gidan su, sai ya garzaya fada, sai ya sami sarki Dawuda Basha a killace, a kwance ba lafiya, ya kamu da annobar shima, bayan yan kwanaki sai ya sami sauki, a cikin wannan halin bayan samun saukinsa ya ci gaba da kokarin lura da sha’anin mulki, duk da raunin jikinsa, ya sa a ka nemo ma’aikata da za su yi aikin kwashe gawarwaki yana biyansu kudi, a lokacin kuwa ko ina cike yake da gawa, gidaje, masallatai, kasuwanni, da hanyoyi.
Sai ya sa ‘yan doka suyi ta aikin tsafatace garin, aka sa lada akan kowacce gawa in mutum ya dauke, sai aka ringa kwashe su ana jefa su kogin Dijla (Tigris river) ba maganar wanka balle likafani.
Mafi yawan gawarwakin ana daure kafarsu ne a jikon bindin dabbobin da ba a san masu ita ba sai a kada ta zuwa kogin tana jan gawar har cikin kogin.

Daga littafin (lamahatun ijtima’iyya min tarikhil Iraqil hadith) na Dr. Ali Al’wardi.
Vol 1, pg,269-275

YA ALLAH MUN TUBA KA YI MANA MAFITA DAGA WANNAN HALI

ALLAH KA RABA MU DA KUSKUREN FATAWA, MUSAMMAN WADDA KE DA ALAKA DA RAYUWAR BAYINKA, DA HAKKOKIN SU.

Leave a Reply

Top
%d bloggers like this: