You are here
Home > Sashin Hausa >

KARSHEN TIKA-TIKAR SHI’A A NIJERIYA (1) Prof. Labdo

75 Views

KARSHEN TIKA-TIKAR SHI’A A NIJERIYA (1)

Daga SHEIKH PROF UMAR LABDO MUHAMMAD.

‘Yan Shi’a sun kwashe shekaru talatin da motsi, wadanda su ne shekarun samuwarsu a Nijeriya, suna TUFKA DA WARWARA. Duk abinda suka kudure, duk abinda suka fadi, duk abinda suka aikata, sai sun warware shi kamar da dai ba su kudure, fadi, ko aikata shi ba. A yau, ‘yan Shi’ar Nijeriya sun cika wadan nan shekaru suna kewayawa a wuri daya, suna dawurwura, suna hajijya, suna wuju-wuju, suna kaiwa da komowa, suna TUFKA DA WARWARA. A cikin wadan nan shekaru babu abinda suka cimma sai baya, babu abinda suka tsinana wa kansu balle wani. Idan kana neman hujja a kan “Bacin Tafarkin ‘Yan Shi’a Da Aqidojinsu” to sai ka shafa Fatiha ka koma gida.

TUFKA DA WARWARA ta farko da suka yi ita ce musun cewa su ‘yan Shi’a ne kwata-kwata. Ina zaton malami na farko da ya ja hankali ga cewa ‘yan Shi’a, wadanda a lokacin suke kiran kansu Burazu, shi’ar suka durfafa shi ne Shaihu Abubakar Mahmoud Gumi, Allah ya gafarta masa. Na biyu shi ne Shaihu Aminuddin Abubakar, Allah ya rahamshe shi. Wadan nan malamai biyu sun yi nasiha ga ‘yan Buraza cewa alakarsu da kasar Iran babu inda za ta kai su sai kudure aqidar shi’anci. ‘Yan Shi’a fafur suka ce ba su yarda ba, sharri ake musu. Suka yi ta zage-zage, kamar yadda suka saba, suna cewa an yi musu kage, su ba sa shi’a, su gwagwarmaya suke yi, kuma babu abinda ya hada su da Iran sai jihadi da yakar Amurka da Israila da Dagutu. Ba’a jima ba ‘yan Shi’a suka komo suna rawar banjo a kan tituna, suna kirarin cewa su ‘yan Shi’a ne, kuma shi’anci shi ne addinin gaskiya. Wannan ita ce TUFKA DA WARWARA ta farko da ‘yan Shi’ar Nijeriya suka yi. Kuma wannan yana nunawa a fili cewa, a lokacin da suke ta musantawar can imma yaudarar su ake yi ba su san abinda suke kai ba, wa imma karya suke wa mutane. Ala kulli halin, wannan TUFKA DA WARWARA tasu tana tabbatar da Bacin Tafarkinsu.

Babbar TUFKA DA WARWARA ta biyu da ‘yan Shi’ar Nijeriya suka yi ita ce a fagen yaki da Dagutu. Ma’anar Dagutu na da fadi a tafarkin shi’anci, amma abubuwan da suka fi lakkanawa wannan suna su ne gwamnati da dukkan rassanta da ma’aikatanta, musamman jami’an tsaro na soja da ‘yan sanda. Haka nan bangaren shari’a da kotuna, musamman kotun majistare. Saboda tsananin kiyayyar ‘yan Shi’a ga kotuna da majistarori har harin ta’addanci suke kai musu. ‘Yan Shi’a sun sha kai hari kotu, alkali na tsaka da shari’a, su sa duka, su kubutar da ‘yan uwansu dake gurfane a gaban kotun, mai shari’a ya sha da kyar.

Amma a yau, ‘yan Shi’a masu TUFKA DA WARWARA, sun komo wai a kotun Dagutu suke neman a yi musu adalci! Har homa suke yi, suna bugun kirji, wai kotu ta ce a saki jagoransu! Suna gwabawa wanda ya ki bin umarnin kotu cewa shi mai mulkin kama-karya ne! Ya isa abin kunya da kaskanci ga ‘yan Shi’ar Nijeriya a ce yau suna neman taimako, suna barar alfarma a wajen kotun Dagutu. Wadanda suka ga jiya, suka ga yau, suka san karyar da ‘yan Shi’a suka rika yi ta yakar kotunan majistare, kai har ma da kotunan Shari’a masu rawani, shi’a ta fadi warwas a gabansu, sun fahimci cewa gaba dayan harakar shi’a da gwagwarmayarta dama wani wasan kwaikwayo ne da wasu yara suka shiga, ko aka shigar da su, kuma babu abinda wannan wasan kwaikwayo ya janyowa al’umma sai asarar duniya da ta addini.

Daga cikin wadanda ‘yan Shi’a ke lankayawa sunan Dagutu akwai sarakan gargajiya. Sarakuna sun sha tasku da bone a hannun ‘yan Shi’a, kama daga zagi da tsinuwa zuwa hari da makami. Suna zagin sarakai a gabansu, a kan kunnuwansu, suna ce musu masu kahon tsumma (suna nufin filafilan rawunansu). Har mai alfarma Sarkin Musulmi bai tsira ba daga ta’annutin ‘yan Shi’a. Sun kai hari da duwatsu ba sau daya ba a kan mai martaba Sarkin Zazzau da wasu sarakunan. Sun terewa mai martaba Sarkin Kano hanya, suka tilasta masa ya ratse don madugunsu ya wuce. Sun yi haka saboda raini da wulakanci ga sarakan gargajiya.

Amma a yau ‘yan Shi’a sun yi kwana, sun zaga sun zagayo, SUN TUFKA SUN WARE, wai su ne ke da’awar son sarakuna da mutunta su. Har ziyara suke kaiwa fadojinsu, suna gaishe su, suna neman albarka! Dan Shi’a rasa kunya beran danga! Wai yau a wajen Dagutu ake neman albarka! Wani Farfesa nasu me yi musu farfaganda har da’awa ya yi cewa wai Gidan Dabo (gidan sarautar Kano) gidan shi’anci ne, wai Sarki wane da wane ‘yan Shi’a ne, don tsabagen rashin kunya da fitsara! To a shekarun baya da suke ce musu Dagutu ba su san ‘yan Shi’a ba ne sai yanzu da tusa ta kure wa bodari?

Amurka ita ce babbar kasar Dagutu a dunaya, a ganin ‘yan Shi’a, don haka suka shafe shekaru masu yawa suna daga murya da kirarin “Death to America” (mutuwa ga Amurka). Koda yaushe suka fito zangazangarsu ta wasan kyaikwayo da gararambarsu da tattaki, suna kone tutar Amurka ko su shimfida ta a kasa su taka ta, su yi rawa a kan ta, saboda was suna kin Amurka kasar Dagutu wacce a wani yayi suke ce mata “Babban Shedani”.

Sai ga ‘yan Shi’a sun yi cikakkiyar kwana daga gabas sun komo suna duban yamma! Gaba dayan TUFKARSU ta shekara talatin da ‘yan kai SUN WARWARE!! Wai yau ‘yan Shi’a ke zuwa ofishin jakadancin Amurka dake babban birnin Tarayya Abuja don neman alfarmar Babban Shedani ya sa baki a sakar musu jagoransu. Wannan yana tabbatar da cewa ‘yan Shi’a da gangan suke, dama karya suke ba wani Dagutu da suke yaka, wargi dai na sukai ‘yan nema (na ari ta bakin Malam Bello Yabo), ba gwagwarmaya, ba yakar Dagutu, ba kafa Gwamnatin Musulunci, ba yakar Israila, ba ‘yanto Palasdinu da masallacin Baitul Maqdis.

‘Yan Shi’a sun shekara talatin da wani abu suna TUFKA DA WARWARA. Ba su tsinanawa kansu kome ba ballantana wani. Ba su ga stuntsu ba su ga tarko, ba addini ba addiila, sai zage-zage, da tsine-tsine, da yawace-yawace, da fada ba cikawa.

Mu kwana a nan.

Leave a Reply

Top
%d bloggers like this: