You are here
Home > Sashin Hausa >

Duk dan Nijeriya yana da yancin zama a ko ina – Sarki Sanusi

139 Views

Sarkin Kano Alhaji Muhammad Sanusi ya nuna goyon baya ga dokar kau da manufar da ke nuna wasu a matsayin baki wanda ke a fadin jihohin kasar. Sarkin wanda yayi magana a bikin cika shekara goma da nadin sarkin kabilar Igbo na Kano, Igwe Boniface Ibekwe, ya bayyana ra’ayinsa cewa yan Najeriya suna bukatar yanci iri guda wajen tabbatar da zaman lafiya, nasara da cigaba. Ya bayyana cewa yan Najeriya suyi ma junansu da’a a jihohin da suke da zama ba tare da yin la’akari da yare, addini da kuma jihohinsu na asali ba. “A Kano, bamu san da batun yan jiha na asali da wadanda ba yan asalin jihar ba. An gina wannan birnin ne kuma arzikinta da ingancinta sun kasance akan budaddiyar yanayinta da masaukinta.” Ya bayyana cewa mutanen Kano ba su da nuna kyashi ko babancin yare ko na addini, inda yake jadadda cewa mutanen Kano na yanzu yawancin mutane ne wadanda asalinsu sun fito ne daga Gobir, Nupe, Kanuri, Baburu, Jukun, da Wukari.

Ya mika godiya ga mai bikin da kuma sauran sarakunan gargajiya na sauran kabilu a jihar kan kokarin da suke yi wajen karfafa zaman lafiya tsakanin kabilu daban daban dake da zama a jihar.

YAKAMATA KA KARANTA: Nijeriya zata fada cikin…..Dahiru Bauchi

Ya bukaci al’umman Igbo da su cigaba da zaman lafiya tare da sauran yan Najeriya a jihar, inda ya jadadda cewa “Mu yan Najeriya ne, mu kuma mun kasance yan adam masu fuskantar kalubale iri guda.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta African Maestro Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.andromo.dev661623.app938722

Leave a Reply

Top
%d bloggers like this: