You are here
Home > Sashin Hausa

An gano dalilin hauhawar fyade a Nigeria

Pauline Tallen, Ministar kula da harkokin mata ta Najeriya ta alakanta hauhawar fyade da dokar kulle da aka saka don dakile yaduwar annobar korona a Najeriya. Tallen ta sanar da hakan ne ga manema labaran gidan gwamnati a ranar Laraba, 10 ga watan Yunin 2020, bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya inda ta kawo matsalar fyade gabansu. Ta bayyana cewa za a dauki mataki wanda zai hada da na shari'a da kuma kafafen yada labarai don shawo kan matsalar fyade. "Fyade ya yawaita a yayin da ake kulle sakamakon annobar korona. Na san ana samun matsalar fyade a kasar nan amma yanzu ta fi yawaita saboda zaune da ake a gida, an rufe mata da yara tare da masu

KUSKUREN MALAMAI NA IYA JEFA QASA DA DUBBAN MUTANE GA HALAKA . ANNOBAR GARIN BAGADAZA DA TA AUKU A SHEKARA TA 1831ad=1246ah, kusan bata da banbanci da covid 19… Dr Zarewa

Wannan annoba da ta faru a garin Bagadaza ta canza komai daga mahallinsa, sai da ta mayar da garin Bagadaza tamkar leda a cikin guguwa. Ana iya cewa wannan annoba ita ce annoba mafi firgici da garin bagadaza ya hadu da ita a tsawon tarihi, wadanda Allah ya yiwa tsawon rai suka tsira daga wannan annobar sun jima suna ba da labarin irin barnar da wannan annoba ta yi. A yanzu haka akwai wata kasuwa a garin Bagadaza da ake kira kasuwar Ja’ifa (kasuwar mussa), dalilin kiranta da wannan suna, shi ne cikar da tayi fal da gawarwaki lokacin wannan annobar, inda ba abin da ke tashi sai warin gawa. Wannan annoba ta fito ne daga arewancin Bagdaza, a watan Yuli na

‘Yan kungiyar masu magunguna a Kano za su rufe shagunansu

Daga MUSA DISO Shugaban qungiyar masu saida magunguna, Nigerian Association of Patent and Propriotory Medicine Dealers (NAPPMED), reshen jahar Kano, Alhaji Husaini Labaran Zakari yace sun umurci 'ya'yan kungiyarsu da su kauracewa bude shagunansu saboda irin cusgunawa da jami'an hukumar KAROTA take musu, wanda a cewarsa, basu da hurumin yin hakan a doka, ganin abinda ake musu ya zama rashin adalci a garesu shi yasa suka xauki wannan matakin. Alhaji Husaini Zakari ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, yace bayan haka ma akwai wasu ma'aikata da ake ajiye wa a bakin kasuwa da haka kawai suke kama musu kaya. Duk da cewa ana gina musu kasuwa ta musamman da za su koma, amma ko

Babban Bankin Najeriya ya hana kudin shigo da madara kasar

Babban bankin Najeriya, CBN, ya sanya madara da dangoginta cikin kayayyakin da ba zai bayar da rangwamen dala ga 'yan kasuwa domin siyo su a kasashen waje ba. Sai dai kuma bankin ya cire wasu kamfanoni shida daga cikin wadanda ya sanya wa wannan takunkumi. A cikin wata sanarwa da babban bankin ya wallafa a shafinsa na intanet, ya ce "A wani bangare na kokarin kara bunkasa samar da madara da dangoginta a Najeriya, CBN ya zabi wasu kamfanoni da za a horar da ma'aikatansu yadda za a rinka samar da madara a cikin gida mai kyau da karko." Babban bankin ya zabi wasu kamfanoni da su kadai aka lamuncewa shigo da madara da dangoginta wadanda suka hada da: Friesland Campina WAMCO Nigeria Chi Limited TG Arla

An sake nada Sudais shugaban Masallatan Harami biyu tsawon shekara 4

Sarki Salman na Saudiyya ya fitar da wata sanarwa ta tsawaita nadin Sheikh Abdul Rahman Al-Sudais a matsayin Shugaban masallatan Harami biyu na tsawon shekara hudu. Kafar yada labarai ta intanet ta Saudi Gazette ta ruwaito cewa Sudais ya yaba wa Sarki Salman da Yarima Muhammad Bin Salman saboda sake aminta da shi kan wannan matsayi yana mai cewa fadar na samun kulawa daga masu mulki. ''Wannan ya taimaka wa fadar wajen tafiyar da ayyukanta cikin sauki da kwarewa. ''Hakan kuma ya yi dai-dai da kulawa da kuma bibiyar harkokin tafiyar da Masallatan biyu masu tsarki da kuma masu ziyartarsu wanda ya ke biyan muradun jagoranci a kasar.''

Top